Rundunar Sojin Saman Najeriya Na Binciken Kisan Farar Hula 2 | VOA Hausa

Shelkwatar rundunar sojojin saman Najeriya ta fara binciken zargin da
ake wa jami’an ta, na kashe wasu fararen hula biyu a jihar Sokoto. Kakakin rundunar Iya Kwamando Ibikunle Daramola, ya shaida hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, cewa rundunar sojin sama ba zata amince da batun danne hakkin bil adama ko rashin da’a da ya shafi jami’anta ba.

Daramola yace an kaddamar da bincike don fayyace abin da ya faru, da irin rawar da sojojin suka taka, kuma muddin an same su da laifi, to tabbas za a dauki kwararan matakai akan su.

A cewar wani masanin harkar sojin sama, Wing Commander M. Salman, domin irin wannan yanayi aka kafa kotun soji, wacce zata gudanar da shari’a idan har an sami jami’an da laifi.

Wannan matsalar dai tuni ta fara jan hankalin lauyoyin kare hakkin bil adama, irin su Lauya Yakubu Saleh Bawa, wanda yace zasu sa ido don ganin yadda binciken zai kasance.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...