Rundunar sojin Najeriya ta kori wasu sojoji 6 daga aikin bisa zarginsu da guduwa daga wajen wani waje da Boko Haram ta kai.
Sojojin da ke aikin yaki da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas, da aka fi sani da Operation Lafiya Dole, an ce sun gudu ne daga wajen wani harin da ‘yan Boko Haram suka kai a kusa da garin Damboa da ke jihar Borno.
Daya daga cikin majiyoyin ta kara da cewa an kashe sojoji sama da 10 a yayin harin. Sai dai har yanzu rundunar sojin Najeriya ba ta tabbatar da harin.
Majiyar da ta zanta da ƴan jarida ta ce an kori sojojin shida ne saboda janyewa daga fagen daga.
Sai dai majiyar ta bayyana hukuncin da aka yi wa takwarorinsa da cewa bai dace ba, inda ta ce sun bar fagen daga ne bayan sun karar da harsashi a artabun da suke yi da ‘yan ta’addan.
A cewar majiyar, ba a tanadar musu isassun makamai da alburusai don yakar ‘yan ta’addan Boko Haram ba; don haka ba a jima ba harsashi ya kare.