
Kocin tawagar kwallon kafar Najeria, Gernot Rohr ya ce dan wasan Chelsea, Tammy Abraham da Fikayo Tomori ba sa cikin tsarin yan wasansa a yanzu.
Abraham mai shekara 21, bai yanke fatan buga wa Super Eagles tamaula ba, tunda mahaifinsa dan Najeriya ne, duk da yi wa matasan Ingila wasa biyu.
Tomori mai shekara 21, wanda aka haifa a Canada ya buga wa matasan tawagar Ingila wasa 15, ya kuma ce idan karfinsa ya kai yana son yi wa Nigeria kwallo tunda iyayensa ‘yan can ne.
Tawagar kwallon kafa ta Ingila za ta kara da Jamhuriyar Czech da Bulgaria a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a cikin watan Oktoba.
Da zarar sun buga wa Ingila wasan babu damar su buga wa Najeriya kwallo kamar yadda hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta fayyace a dokarta.
Najeriya ta taba rarrashin ‘yan wasa da suka buga wa Ingila wasannin matasa kamar su Aina da kuma Sone Aluko sannan suka yi wa Super Eagles kwallo.