Rikici ya sake barkewa tsakanin ‘yan sandan Isra’ila da Falasdinawa a harabar Masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus a daidai lokacin da Falasdinawa ke ibadun neman yin gamon katar da daren lailatul kadri.
Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross a yankin Falasdinu, ta ce fiye da mutane 90 ne suka jikkata galibi kananan yara wadanda harbin harsashen roba da gurneti mai sa kwalla ya raunata.
Wannan dai shi ne rikici mafi muni da aka taba gani a ‘yan shekarun baya-bayan nan a yankin, a ci gaba da ke Allah wadarai da matakin Isra’ila na korar Falastinawa don gina wa Yahudawa matsuguni a binrin Kudus da Falasdinawa ke yi.