Real Madrid za ta fafata da Valencia

Real Madrid

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Real Madrid, a ranar Laraba, za ta ziyarci Valencia domin karawa da Valencia a wasan mako na 30 a gasar La Liga da za su kara.

Tuni Zinedine Zidane ya bayyana ‘yan wasa 19 da zai je da su karawar da za suyi afilin wasa na Mestalla.

A wasan farko da suka yi a Santiagio Bernabeu ranar 1 ga watan Disambar 2018 a bana, Madrid ce ta yi nasara da ci 2-0.

A kakar bara da kungiyoyin biyu suka kara a La Liga, sun tashi 2-2 a wasan farko da aka yi a Bernabue ranar 27 ga watan Agustan 2017, inda Real ta ci karawa ta biyu 4-1 ranar 27 ga watan Janairun 2018.

Real Madrid tana ta uku a kan teburin La Liga da maki 57, yayin da Valencia tana ta bakwai da maki 43.

‘Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Navas da Luca da kuma Moha.

Masu tsaron baya: Vallejo da Ramos da Varane da Marcelo da Odriozola da kuma Reguilón.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Asensio da Isco da kuma Ceballos.

Masu cin kwallaye: Mariano da Benzema da Bale da kuma Lucas Vázquez.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...