Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Real Madrid na son ba Manchester United fam miliyan £90 hadi da Gareth Bale, mai shekara 30, domin karbo Paul Pogba.
Sai dai ta bukaci dan wasan tsakiyar na Faransa ya tabbatar da yana kan ganiyarsa da nuna kwazo a fili. (El Desmarque, via Express)
Real Madrid kuma na son sayar da Bale da dan wasan Colombia James Rodriguez, mai shekara 28, domin sayo dan wasan Paris St-GermainKylian Mbappe, mai shekara 20. (Calciomercato)
ShugabanReal Madrid Florentino Perez na shirin bin duk hanyoyin da suka dace domin karbo Mbappe zuwa Bernabeu a kasuwar musayar ‘yan wasa mai zuwa. (AS)
Bayern Munich ta fara tunanin karbo dan wasan baya na Athletic BilbaoUnai Nunez mai shekara 20 wanda Arsenal da Evertonsuka nuna sha’awar suna so. (Goal.com)
Masu ba Arsenal shawara kan Mesut Ozil, mai shekara 31, sun son janyo ra’ayin dan wasan ya koma taka leda Amurka a gasar MLS. (Mail)
- Champions League: Messi ya bude sabon babi
- Shin ina dan wasan tsakiyar Arsenal Mesut Ozil yake?
KocinManchester City Pep Guardiola ya ce suna kan nazarin sayo dan wasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz, mai shekara 21, wanda ya kulla yarjejeniya da Aston Villa a bazara. (Manchester Evening News)
Dan wasan Brazil Willian, mai shekara 31, ba ya son komawa kasarsa taka leda bayan kawo karshen yarjejeniyarsa a karshen kaka inda ya nuna sha’awar ci gaba da murza leda a Chelsea. (Metro)
KocinChelsea Frank Lampard yana fatan ‘yan wasan gaba na Ingila Tammy Abraham, mai shekara 22, da Fikayo Tomori za su sabunta kwangilarsu a Stamford Bridge. (Goal.com))