Real Madrid ba za ta sayar da Varane ba, Coutinho zai koma Chlesea | BBC Hausa

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Real Madrid ba za ta sayar wa Manchester City dan wasanta dan kasar Faransa Raphael Varane, mai shekara 26 a bazara ba. (Star)

Juventus ta shirya tsaf domin bai wa Manchester City dan wasan Brazil Douglas Costa, mai shekara 29, a wani bangare na karbo Gabriel Jesus, mai shekara 23 daga City. (Calcio Mercato, in Italian)

Kocin Everton Carlo Ancelotti ya kaddamar da wani gagarumin shiri domin sayo ‘yan wasan Real Madrid Gareth Bale, mai shekara 30, da James Rodriguez, mai shekara 28. (Mail)

Chelsea na tattaunawa da dan wasan Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 27, wanda yanzu haka yake Bayern Munich a matsayin aro daga Barcelona. (Sun)

An shaida wa Manchester United cewa ba su da damar daukar dan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane saboda tsawon wa’adin kwangilar dan wasan mai shekara 26, wacce za ta kare a 2024. (Manchester Evening News)

Manchester United na son dauko Matthijs de Ligt lokacin musayar ‘yan kwallo yayin da rahotanni ke cewa dan kasar ta Netherlands mai shekara 20 na fafutukar saman wurin zama a Juventus. (Express)

Newcastle United bata karaya ba a yunkurin da take yi na dauko dan wasan Lille mai shekara 21 Boubakary Soumare, duk da yake Real Madrid na zawarcin dan wasan na Faransa. (Sport, in Spanish)

Amma ita ma Liverpool tana son sayo Soumare kuma ta soma tattaunawa a kan kwangilarsa. (Teamtalk)

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...