Peter Obi ya yi zargin matsa masa lamba don ya bar Najeriya

Peter Obi

Asalin hoton, Getty Images

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen Najeriya na 2023 Peter Obi ya mayar da martani kan wata murya da ke yawo a shafukan sada zumunta.

Ana zargin cewa muryar na wata tattaunawa ce ta waya tsakanin Obi da shugaban cocin Living Faith, Bishop Oyedepo.

Hakan na zuwa ne bayan kimanin kwana biyar da ɓullar muryar.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na tuwita a ranar Laraba, Obi ya ce ce-ce-ku-cen da ake yi kan muryar wata maƙarkashiya ce da jam’iyya mai mulkin Najeriya ke yi na tursasa masa ya bar Najeriya.

Peter Obi dai ya nesanta kansa da muryar da ake ta yaɗawa a shafukan sada zumunta da kuma jaridun ƙasar.

Muryar dai ta haifar da zazzafar muhawara saboda irin kalaman da ɗan takarar shugaban ƙasar ya yi a cikin wayar, waɗanda ake ganin ba su dace da shi ba.

A cikin muryar da aka naɗa ta wayar tarho, wadda BBC ba ta tantance sahihancinta ba, an ji Obi yana cewa “Daddy, ina son ka yi wa mutanenka na Kudu-maso-yamma da Kwara magana, Kiristoci na Kudu-maso-yamma da Kwara.”

Ya ƙara da cewa “Wannan yaƙi ne na addini.” Inda shi kuma Bishop Oyedepo ya amsa da cewa “Na yarda da hakan, na yarda da hakan, na yarda da hakan.”

Obi ya ci gaba da cewa “Kamar yadda na sha faɗi – idan komai ya tafi daidai, ba za ku yi da-na-sanin goya min baya ba.”

Sai Oyedepo ya ce “Muna nan muna kallon abin da Allah zai yi.”

Martani ga Gwamnatin Tarayya

Bayan fitar muryar, Minisan yaɗa labaru na Najeriya, Lai Mohammed ya zargi Peter Obi da kokarin tayar da husuma tsakanin al’umma.

A wata tattauna da manema labaru a Amurka, Lai ya yi ikirarin cewa kalaman Obi a cikin wayar da ake zargin sun yi da Bishop Oyedepo tamkar ‘cin amanar ƙasa ne.’

Sannan ya ce kalaman Obi da mataimakinsa sun yi kama da na mutane da ke neman mukami ko ta halin ƙaƙa.

Sai dai a martanin da ya mayar, Peter Obi ya ce “Ban taɓa tattauna wani lamari da zai zama zagon-ƙasa ga Najeriya ba; Ban taɓa iƙirari ko kuma goyon bayan wani ya yi kalaman da za su tayar da hankali ba a Najeriya.

Ya ƙara da cewa waɗanda suka ƙirƙiro wannan lamari na amfani da muƙamansu na gwamnati da ƴan korensu domin su shafa masa kashin kaji.

More News

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraɗiyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...