Osinbajo ya nisanta kansa daga ofishin yakin Neman Zaben 2023

Sakatariyar magoya bayan mataimakin shugaban kasar Najeriya
Ofishin yakin neman zabe da wasu masoyan mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbanjo suka bude masa a Abuja

A Najeriya, wasu da suke ikirarin magoya bayan mataimakin shugaban kasar ne sun bude ofishinsu na tallata shi domin ya tsaya takarar shugabancin Najeriya a shekara ta 2023.

Mutanen, wadanda ke karkashin wata kungiya mai suna The Progeressive Project, wato TPP a takaice, sun bayyana cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya cancanci shugabancin Najeriya idan aka yi la`akari da iliminsa da kuma dabi`unsa.

Sakatariyar magoya bayan mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya tsaya takarar shuganbancin kasar a babban zabe mai zuwa ba a boye take ba, kasancewar an girka ta ne a daya daga cikin unguwanni irin na alfarma a Abuja.

Wakilin BBC da ya kai ziyara wurin , ya ce ofishin bene ne mai hawa daya, kuma a cikin harabar an girke hotunan mataimakin shugaban kasar wanda a jikin hotunan an yi rubutun da ke cewa shi ne ya cancanci jagorancin Najeriya a zaben shekarar 2023

Shugabannin kungiyar, sun bayyana cewa dabi`un mataimakin shugaban kasar ne suka ja hankalinsu wajen tallata shi a duniya. Alhaji Musa Gidado shi ne sakataren kungiyar.

” Yadda ya ke bin shugaban kasa sau da kafa kuma shi ne kadai bai da banbanci tsakanin koina a fadin kasar, yana ganin kowa dan Najeriya ne, kuma mai ilimi ne ga hazaka, ga kokari da hakuri, natsuwarsa mu ka gani cewa ya kamata mu sa shi a gaba ya zama shugaban kasa”. in ji shi

Sai dai kungiyar ta yi ikirarin cewa ba bu wani da mataimakin shugaban kasa ya sani a cikin mambobinta kuma tana samun tallafi ne daga masoyansa da yawa

Abinda ofishin mataimakin shugabann kasa ya ce a kan al’amarin

Sai dai bangaren mataimakin shugaban kasar ya ce ba shi da wata alaka da wadanda suka bude sabuwar sakatariyar.

Mai taimakawa shugaban kasa a kan harkokin kananan masana’antu a ofishin mataimakin shugaban kasa Alhaji Abdurrahman Bappa Yola ya ce masoya Farfesa Yemi Osinbajo suka tara kudi domin bude masa ofis.

“Wannan abu ne wanda masoya ne kuma su ke ganin ya dace, ya cancanta su ke yi wadanan abubuwa amma shi bai fito ya furta yana cikin wannan takara ba, kuma yana da maigida shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ba bu wani abu da ke gabansa illa su ga sun sauke nauyin da al’umma su ka dora mu su”. in ji shi

Duk da cewa bangaren mataimakin shugaban kasar ya nuna ba shi da nasaba da kungiyar mogoya bayan nasa, masana harkokin siyasa a bangare guda na fassara bullar irin wannan gangami na magoya baya da cewa wani salo ne na bugun juji domin a ji karar gwazarma, wato ma`auni ne na irin tagomashin dan siyasa a wajen iyayen gidansu da kuma sauran jama`a.

Tuni dai Su ma magoya bayan jigo a jam`iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, wanda ubangidan siyasar mataimakin shugaban kasar ne, sun kaddamar da nasu ofishin na goyon bayan ya tsaya takarar shugabancin Najeriyar.

Ko da yake bai fito fili ya ce zai tsaya ba.

A yanzu `yan Najeriya sun zuba ido su ga yadda wannan zarwarcin mulkin kasar zai kaya tsakani da da uba amma irin na siyasa.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...