NDLEA ta kwace miyagun kwayoyi na naira miliyan 80 a Abuja

Hukumar NDLEA dake yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ce jami’anta dake Abuja sun samu nasarar kwace kilogram 3900 na miyagun Æ™wayoyi da darajarsu ta kai naira miliyan 80 a cikin watanni huÉ—u na karshen wannan shekarar.

Kabir Tsakuwa kwamanda a hukumar shi ne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja.

Ya ce miyagun kwayoyin da aka kwace sun haÉ—a da hodar ibilis ganyen tabar wiwi, Metamphetamine, kwaÆ´ar Tramadol, Diezapam da kuma Rophynol.

Ya kara da cewa jumullar mutane 134 aka kama da ake zargi da sha, safara da kuma sayar da miyagun kwaÆ´oyin.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...