NDLEA ta kama tan 3.6 na miyagun ƙwayoyi a Kano

Hukumar NDLEA dake yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi reshen jihar Kano ta kwace tan 3.6 na haramtattun miyagun kwayoyi a jihar cikin watanni uku.

Abubakar Idris-Ahmad kwamandan hukumar na jihar Kano ya ce mutane 241 aka kama a tsakanin watan Yuli zuwa Satumba.

Ya ce kwayoyin da aka kama sun haɗa da tan 3.4 na ganyen tabar wiwi kilogram 274.1 na Codeine da Tramadol sai kilogram 0.4 na hodar ibilis nau’in cocaine sai nau’in heroin da metamphetamine.

Idris ya ce hukumar ta kuma yi nasarar samun hukuncin ɗaure masu safara da kuma ta’ammali da miyagun kwaƴoyi su 18 cikin 29 da ta gurfanar a gaban kotu a cikin watanni uku.

Ya kara da cewa har yanzu akwai sauran kararraki 132 da suke gaban kotu

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faɗa tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...