NDLEA TA Kama Kwayar Tramadol Miliyan 7.5 Filin Jirgin Saman Lagos

Hukumar NDLEA dake hana sha da da fataucin miyagun kwayoyi ta ce jami’anta dake filin saman Murtala Muhammad dake Lagos sun kama kwayar Tramadol miliyan 7.5.

A wata sanarwa ranar Lahadi, Femi Babafemi mai magana da yawun hukumar ya ce yinkurin gungun wasu batagarin mutane na shigo da kwayar Najeriya ya gamu da tasgaro sakamakon dakile yinkurin da jami’an na NDLEA da hadin gwiwar jami’an kwastam suka yi.

Ya ce an kwace kunshin kayan ne ranar 22 ga watan Disamba bayan da jirgin Turkish Airlines ya kawo su ba tare da an rubuta kasar da aka yi su ba ko kuma kamfanin da ya samar da su.

Mai magana da yawun hukumar ya ce wannan ne karon farko da aka samu kwace irin wannan kayan a jirgin da ya fito daga birnin Hamburg na kasar Jamus.

Ya kara da cewa Tramadol din mai karfin 225mg an tsara su a fakiti na musamman da aka rubuta tamol-x aka kuma boye su a manyan katan guda 100 masu nauyin 715Kg.

More from this stream

Recomended