Nasir El-Rufa’i: Me ya sa aka yi wa gwamnan Kaduna taron dangi a Tuwita? | BBC Hausa

  • Umaymah Sani Abdulmumin
  • BBC Hausa
Bayanan hoto,
Lauyoyi sun cacaki el-Rufai a tuwita

Zargin tauye haƙƙi kusan shi ne abin da ake tafka muhawara a kai kan gwamnan jihar Kaduna Nasir Elrufa’i tun safiyar wannan Juma’ar a shafukan sada zumunta a Najeriya.

Wannan kuwa ya biyo bayan gayyatar da ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa ta yi wa gwamnan domin halartar taronta na ƙasa da ta shirya gudanarwa, wanda ya gamu da suka.

Sai dai abu kamar wasa wannan batu ya zama babba domin tun a jiya Alhamis ƙungiyar Lauyoyin ta sanar da janye gayyatar da ta yi wa gwamnan sakamakon adawar da wasu lauyoyi suka rinka nuna wa.

Wannan batu a yanzu ya kasance abin da ke jan hankali inda wasu ke suka wasu kuma ke yaba matakin ƙungiyar lauyoyin.

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

Kungiyar lauyoyin ta jadada cewa ta yanke wannan hukunci ne biyo bayan zanga-zangar da wasu lauyoyi suka yi kan gayyatar.

Da fari dai wani lauya mai suna Usani Odum ne ya soma ƙaddamar da takardar koke ta intanet inda ya nemi ƙungiyar ta janye gayyatar da ta yi wa gwamnan.

Sannan daga bisani wasu lauyoyi suka rinƙa aike sako cewa za su bijire wa taron in dai El-Rufai na cikin waɗanda aka gayyata domin gabatar da jawabi.

Kauce wa Twitter, 2

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 2

Shi ma Femi Falana babban lauya mai fafutukar kare hakkin dan adam na cikin lauyoyin da wasikar da ya rubuta ta nuna adawa da halarta El-rufa’i a taron ke ta yawo a shafin intanet.

Wasu daga cikin bayanan da ke kunshe a wasiƙar sun hada da zargin cewa gwamnan yana ”bijirewa umarni da raina kotu”. ”Kuma gayyatar irin wadanan mutane ya saɓa dokokin kungiyar lauyoyi.”

Sannan wasiƙar ta kara da cewa ”ƙungiyar ba za ta ragawa masu riƙe da ofisoshin gwamnati da ke da ra’ayin rashin hukunta masu laifi a ƙasa ba”.

Masu ƙoken akasari na zargin gwamnan da gazawa wurin shawo kan rikicin Kudancin Kaduna da kuma take haƙƙn bil adama.

Kuma ragargazar gwamnan da aka rinƙa yi ta tilasta wa kungiyar lauyoyi yanke shawarar janye goron gayyatar da aka tura wa gwamnan.

Sai dai yayin da wasu ke nuna adawa da halartar El-rufai wannan taro wasu lauyoyin kuma cewa suke suna bayan gwamnan.

Kauce wa Twitter, 3

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 3

Halima Gaci ta ce: Na san ba zai sauya wannan abu ba amma dai na janye daga halartar taron lauyoyi ta ƙasa da za a gudanar a intanet saboda janyewar @elrufai a matsayin bakon da zai yi jawabi na musamman kan dalilai da zarge-zarge marasa inganci da hujja #IStandWithElrufai

Amma a nasu bangaren masu sharhi kamar Dr. Hakeem Baba Ahmed ya ce janye gayyatar da aka yi wa gwamnan El-Rufai ta hana shi magana a wajen wannan taro ya saɓa ƙa’idar ƙungiyar da ya kamata a ce ta ƙarfafa ba da dama a saurari mutum da kuma damar yi masa tambayoyi.

Kauce wa Twitter, 4

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 4

Wani Bashir Dabo kuma yana cewa: NBA ta jefa kanta cikin yanayi mara bullewa kan shawarar da ta yanke kan Mal el-Rufa’i. Kungiyar ta ba da kanta kan martabar da take da ita saboda dalilai na siyasa. Ƙungiyar ta shigar da kanta cikin kazamar siyasa irin ta Najeriya.”

Kauce wa Twitter, 5

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 5

Mutane da dama ne suka sanya hannu a ƙorafin buƙatar ƙungiyar lauyoyi na cire sunan gwmanan El-Rufa’i cikin baƙin da za su yi jawabi a taronta na ƙasa da ke soma wa a ranar 24 ga watan Agustan 2020.

Lauyoyin na cewa ƙarƙashin mulkin el-Rufa’i, an cafke mutane da dama ta haramtacciyar hanya, wasu daga cikinsu akwai fitattun masu suka, Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, wanda ya ɓace babu labarinsa.

Tuni da ƙungiyoyin irin su SERAP mai fafutukar kare cin hanci ta ce ta yi marhaba da matakin janye gayyatar da aka yi wa El-Rufai, sannan ta shawarci ƙungiyar kar ta gayyaci ko da mutum guda daga gwamnatin da ‘yan majalisa har sai Shugaba Buhari ya mutunta umarnin kotuna.

Kauce wa Twitter, 6

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 6

Ita ma ƙungiyar ƴan shi’a ta IMN ta yaba wa mataƙin lauyoyin na janye gayyatar da ta yi wa gwamnan a cikin wata sanarwa da kakakinta Ibrahim Musa ya aike wa BBC ranar Juma’a. Sanarwar ta ce gwamnan bai cancanci halartar taron ba.

Sai dai ƙungiyar lauyoyi reshan jihar Jigawa ta yi barazanar cewa babu daya daga cikin mambobinta da za su halarci taron muddin el-Rufa’i ba zai je taron ba.

Kazalika ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi wato Muric ta yi kira ga lauyoyin arewacin Najeriya su kaurace wa taron saboda rashin dacewar da ta ce an yi wa gwamnan.

Wasu labaran da zaku so karantawa

Martanin El-Rufai

Gwamnatin Kaduna ta wallafa a Tuwita amincewar gwamna El Rufa’i da goron gayyatar da NBA ta yi wa gwamnan na Kaduna bayan ƙungiyar lauyoyin ta janye gayyatar.

Sannan gwamnatin ta mayar da martani ga matakin janye gayyatar inda ta ce bai kamata babbar ƙungiya kamar NBA ta amince da wani zance ba daga wani ɓangare kan batun da ya shafi ƙasa ba.

Gwamnatin ta ce kalaman ɓata suna da wasu mambobin ƙungiyar suka yi wani abu ne na daban kuma za ta mayar da martani.

Zuwa yanzu gwamnatin Kaduna ko Gwamna El Rufa’i ba su mayar da martani ba ga ƙungiyar ƴan shi’a.

Sharhi

Wannan yanayi da ake ciki na nuna alamomin rarrabauwar kawuna tsakanin lauyoyi da wasu masu sharhi.

Yayin da ake gani kamar kusan taron dangi aka yi wa el-Rufai a shafukan sada zumunta, wasu nuna goyon baya suka yi da nanata cewa suna ɓangaren gwamnan.

Yanzu abin jira a gani shi ne yadda wannan ce-ce-ku-cen zai wanye tsakanin lauyoyin, ko da yake akwai masu cewa siyasa ta shiga zance.

Sannan akwai masu cewa idan har za a hana el-Rufai zuwa taron to kamata ya yi wannan hukunci ya hau kan gwamnan Nyesom Wike na Ribas domin halayensu na da kamanceceniya.

Karin wasu labarai da za a iya karantawa

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...