Najeriya za ta daukaka kara kan shari’arta da P&ID a Birtaniya

Muhammadu Buhari

Hakkin mallakar hoto
Buhari Sallau

Gwamnatin Najeriya ta ce tana duba yiwuwar kama wasu jami’ai da ta ke zargi da hannu a wani hukuncin kotun Birtaniya da ya bukaci sai ta biya wani kamfani tsabar kudi har dala biliyan 9, saboda saba yarjejeniya da suka kulla.

Wata kotun London ce ta umarci gwamnatin Nijeriya a ranar Juma’a ta biya kamfanin Process & Industrial Developments Ltd (P&ID) wadannan makudan kudi ta hanyar kwace kadarorinta.

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu, ya ce batun tsohuwar shari’ah ce da jami’an gwamnatocin baya suka gaza wajen daukaka kara, har damar ta rufe.

“Masu mulki a wancan zamani ba su daukaka kara ba har kofa ta tsoshe,” in ji shi.

Ya kuma ce gwamnatin Buhari ta yi kokarin tunanin matakin da za ta dauka don jinkirta aiwatar da hukuncin domin bude kofar ta daukaka kara amma kotun a Ingila ta ce ba zata bayar da wannan dama ba.

Ya zargi jami’an gwamnatin baya da yin sakaci kan abin da ya kira hadin bakinsu don a cuci Najeriya har suka bari abu ya kasance haka.

Ya ce duk da gwamnati za ta daukaka kara amma abu na farko da za a yi shi ne duk wani wanda aka san da hannunsa a cikin wannan hadin baki don a cuci Najeriya tare da wani kamfani na kasar waje, gwamnati za ta sa a kamo su kuma za ta dauki mataki akansu.

Wata sanarwa a shafin intanet na kamfanin ta ce yarjejeniyar ta ba shi damar gina wata katafariyar masana’ntar gina sarrafa iskar gas wadda Najeriya za ta karba kyauta don bunkasa lantarki a kasar.

Amma kamfanin ya ce ya fuskanci karin kudin ruwa a kullum saboda rushewar yarjejeniyar, batun da lauyoyin gwamnatin Najeriya suka ce ya wuce hankali.

Tun farko a 2017 kotu ta bukaci Najeriya ta biya kamfanin kusan dala biliyan shida da rabi kafin yanzu kuma kotun London ta kara dala biliyan biyu da miliyan dari hudu.

jimillar kudin dai ta kai kwatankwacin kashi 20 cikin 100 na dukiyar da Najeriya ta ce ta tara na lalitar kudadenta na kasashen ketare wato dala biliyan 45.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...