Najeriya Ta Sami Maganin Coronavirus Daga Rasha

Wata sanarwa mai dauke daga mai kakakin ma’aikatar lafiya ta Najeriya Olujimi Oyetomi, ta ce Jakadan kasar Rasha a Najeriya Alexey Shebarshin ne ya hannunta wa Ministan Lafiya na Najeriya Osagie Ehanire ragakafin, a lokacin wata ziyara da ya kai a ma’aikatar ta lafiya da ke Abuja.

Sanarwar ta ce za a hanzarta mika rigakafin ga hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna, NAFDAC, da cibiyar Binciken Magunguna ta Najeriya da wasu hukumomin da lamarin ya shafa, don tabbatar da ingancin maganin kafin a duba yiwuwar amfani da shi.

A kwanakin baya ne shugaban Kwamitin musamman na Shugaban kasa akan yaki da cutar COVID-19ya, ya ce sun fara yin gwajin wasu magunguna a kokarin dakile yaduwar cutar ta coronavirus, inda ya kara da cewa an riga an ke6e rukuni 22 da ke yankunan 13 na kasar domin gudanar da gwajin maganin.

Hukumar dakile Yaduwar Cututtuka ta kasa, NCDC, ta ce an sami sababbin kamuwa da cutar ta COVID-19 156 a fadin kasar.

Wannan lamarin ne ya sa Shugaban Kwamitin na musamman, kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Gida Mustapha ya ba da shawara da kakkausar murya cewa mutane su rika biyayya ga dokokin kariya domin cutar tana nan ba ta tafi ko ina ba.

Boss Mustapha ya yi gargadi cewa cutar tana ci gaba da kashe mutane musamman a kauyuka da dama saboda har yanzu wasu ba su yarda cewa cutar tana yaduwa a kasar ba.

Amma duk da haka ya ba da tabbacin cewa za’a cigaba da wayar da kan jama’a ta kafafen yada labarai a kokarin shawo kan cutar.

More from this stream

Recomended