Najeriya: Sama da mutane miliyan daya ne ke ba-haya a sarari – UNICEF | VOA Hausa

Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya yace ‘yan Najeriya miliyan 47 ne wato kashi 24 cikin dari ke bayan gari a fili ko a makewayi marar inganci a binciken data gudanar a shekarar 2018.

UNICEF ta bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai da aka gudanar a jihar kano kan batun tsaftar muhalli ta hanyar yaki da bayan gari a fili.

Dangane da wannan lamarin, mataimakin daraktan bincike da sa ido na ma’aikatar kula da muhalli na Abuja Hassan Abubakar yace wannan dabi’ace marar kyau wadda tu’ammali da miyagun kwayoyi ke haifar wa, kuma ma’aikatar na hukunta duk wadda aka samu yana aikata hakan.

Shima a nashi bayanin, jami’in tsafta na ma’aikatar kula da muhalli a Abuja Simeon Ajueyitsi yace suna fuskantar karancin baddaki na jama’a a birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Dakta Lawal Musa Tahir wani likita da Sashen Hausa ya yi hira da shi dangane da batun yace ba haya a fili na kan gaba wajen yaduwar cututtuka kamar amai da gudawa, zazzabin Tyhoid, ciwon hanta da sauran su.

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin kokarinta don ganinan kawo karshen bayan gari a fili zuwa shekara ta 2025.

More News

Kotu Ta Hana PDP Cire Shugaban RiÆ™on Jam’iyar

Wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta hana jam'iyar PDP dakatar da Umar Damagum daga matsayinsa na shugaban riƙon jam'iyar. Mai Shari'a  Peter Lifu shi...

Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki Da Ya Kai  Saudiya da Nezaland

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland. A ranar 22 ga watan Afrilu ne...

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...