NAHCON Ta yi ƙarin dala $250 kan kuɗin kujerar aikin hajjin bana

Zikirillah Hassan, shugaban hukumar Aikin Hajji Ta Kasa, NAHCON ya ce kamfanonin jiragen sama da aka amince su ɗauki alhazan bana zuwa kasar Saudiyya sun amince ayi karin dala $250 kan kuɗin kowace kujera.

Shugaban ya bayyana haka ne a Abuja ya yi wani taron horarwa da aka shiryawa ma’aikatan NAHCON, na hukumomin alhazan jihohi da kuma na masu zaman kansu da aka fi sani da yan jirgin yawo.

Hassan ya tabbatar da cewa kuɗin karin ba zai fito daga hannun alhazan ba.

Ya ce kamfanonin jiragen saman Air Peace, Max Air,Azman da kuma Aero Contractors su ne suka gabatar da wannan bukatar saboda rikicin da ake fama da shi a kasar Sudan wanda ya jawo karin lokaci mai tsawo kafin a isa Saudiyya.

Tun kafin wannan karin mutane da dama sun koka kan yadda kuɗin kujerar aikin hajjin bana ya ƙaru sosai.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani ɓangare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...