Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta haramta shigo da taliyar Indomie zuwa Najeriya.
A wata zantawa da ta yi da manema labarai a ranar Litinin, Darakta Janar na Hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana hakan.
Hukumar ta NAFDAC ta dauki matakin ne biyo bayan wani bincike da hukumomin Taiwan da na Malaysia suka gudanar, inda ta ce an gano sinadarin ethylene oxide mai haddasa cutar daji a cikin taliyar.
Shugaban hukumar ta bayyana cewa akwai abin dubawa al’amarin ethylene oxide kuma tuni aka tuntubi daraktan kula da ayyukan dakin gwaje-gwajen abinci kuma yana aiki kan hanyar tantancewa game wannan batu.