‘Na sha tsangwama bayan an zarge ni da coronavirus’

Wani makusancin Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, Alhaji Bello Abdullahi Badejo ya ce shi da iyalinsa sun sha tsangwamna bayan an debi samfurin jikinsa don gwajin cutar covid-19.

Badejo wanda jagora ne na kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ya ce ya shiga halin firgici bayan an zayyana shi a matsayin daya daga cikin wadanda za a yi wa gwaji saboda kusancinsu da gwamnan Bauchi

A cewarsa, Bala Mohammed wanda gwamnatin jihar Bauchi ta yi karin haske cewa yana samun waraka a wurin da aka kebe shi, abokin mu’amalarsa da kusan ko yaushe sukan yi hulda.

Ya ce duk da gwajin da aka yi masa ya nuna ba ya dauke da cutar, amma yana fuskantar tsangwama a wajen mutane.

Ya ce wasu har sun rika bi suna yada cewa “an killace gidana an hana mu fita (ni da iyalina) gaba daya.”

“Wani ma zai kira ka a (waya) sai ya bakam ya yi shiru ya ji (bugawar numfashinka), wani kuma zai kira ka ya ji ko lafiya kake,”

“Wani sai da ma ya zo har wajenmu yake cewa min ai an fada masa cewa ina tare da gwamna an killace mu waje daya amma ni wai na gudu, kamar yadda aka ba shi labari ban ma iya zama wurin ba,” in ji Badejo.

Cutar coronavirus da ke shafar numfashi na ci gaba da zama alakakai a duniya kuma kawo yanzu ba a sanar da maganin cutar ba.

A duniya, coronavirus ta harbi sama da mutum miliyan daya tare da sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 60,000, a cewar Jami’ar Johns Hopkins.

Amurka na da sama da mutum dubu dari uku sai mutum 8,100 da suka mutu a kasar sanadiyyar cutar.

Sai dai a Najeriya, cutar ta harbi mutum 214 sai mutum 25 da suka warke daga cutar yayin da mutum hudu kuma suka mutu.

Toh ya ya mutanen da aka debi samfurin jininsu domin yi musu gwaji ke ji kuma wane hali suke fuskanta cikin jama’a?

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...