Mutum miliyan 60 ba su iya rubutu da karatu ba a Najeriya | BBC Hausa

Ilimi

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumar samar da Ilimin manya a Najeriya ta ce mutum sama da miliyan 60 daga cikin ‘yan kasar kusan miliyan 200 ne ba su iya karatu da rubutu ba a kowane irin yare.

Sakataren zartarwa na hukumar Farfesa Abba Abubakar Haladu ya ce matsalar ta samo asali ne tun daga lokacin mulkin mallaka inda aka samu gibi a yawan yaran da ke zuwa makaranta.

Farfesa Haladu ya ce kididdigar ta samo asali ne daga kidayar jama’ar kasar da aka yi a shekarar 1991, da kuma yawan karuwar jama’a da ake samu a Najeriya.

Ya kuma ce hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi wani rahoto da ya bayyana cewa kashi 27 cikin dari na mutanen duniya miliyan 750 da ba su iya karatu na kasashen kudu da hamadar sahara.

Kuma Najeriya ce kasar da ta fi sauran kasashen yankin yawan mutane don haka kasonta na mutanen da ba su iya rubutu da karatu ba ya fi yawa.

Ya ce akwai dalilai da yawa da ya sa kason Najeriya ya yi yawa.

A cewarsa “wasu yaran iyayensu ba su da halin kai su makaranta, wasu kuma rashin makarantun ne a yankunansu.”

Ya kuma ce “tafiyar hawainiya da ake fuskanta a fannin bayar da ilimin manya ya jawo wannan.”

Ya ce matsalar ta fi karfin hukumar kuma ya kamata gwamnatocin jihohi da gwamnati tarayya su hada kai don dakile matsalar.

Farfesa Haladu ya ce rashin samun ilimin firamare ya taimaka wajen tabarbarewar rashin iya rubutu da karatu a Najeriya.

Wadannan alkaluma dai sun nuna cewa kusan kashi daya bisa uku na ‘yan kasar ba su iya rubutu da karatu ba.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...