Mutane 6 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Jihar Niger

Matafiya da basu gaza shida ba ne aka bada rahoton sun mutu bayan da wani jirgin ruwan fasinja ya nutse a kogin Zamare a karamar hukumar Agwara ta jihar Niger.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin lokacin da matafiya da yawancinsu manoma ne suke zuwa jihar Kebbi.

Mazauna garin sun fadawa jaridar Daily Trust cewa an gano gawar ɗaya daga cikin matafiyan a yayin da ake cigaba da aikin nemo sauran.

Jirgin na dauke da mutane sama da 20 ciki har da mata da kananan yara ya kuma kife ne bayan da injinsa ya lalace a tsakiyar ruwa kamar yadda ake shedawa wakilin jaridar Daily Trust.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Niger, Garba Salihu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce hukumar bata samu cikakken rahoton kan abin da ya faru ba.

More from this stream

Recomended