Mutane 5 da suka sayar da jariri ɗan wata biyu sun faɗa hannun ƴan sanda

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta ce jami’anta sun kama mutane 5 da ake zargin su da hannu a safarar wani jariri mai watanni biyu.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya ce an samu nasarar kamen ne biyo bayan korafi da rundunar ta samu na ɓatan yaro jariri.

Hundeyin ya ce mahaifiyar jaririn ce ta kai ƙorafin cewa wata mata mai suna Gloria Sunday ta gudu da ɗanta zuwa wani wuri da bata sani ba a ranar 11 ga watan Yuli.

“Ƴan sanda masu bincike sun duƙufa aiki har ta kai ga kama Gloria Sunday wacce a lokacin bincike ta amsa sayar da jaririn ga Fasto Peter Uboh kan kuɗi naira ₦500,000,” a cewar sanarwar.

Sanarwar ta cigaba da cewa shi kuma Fasto Udoh  ya sayar da jaririn kan kuɗi miliyan 1,450,000 ga wata mata mai suna Loretta Nelson wacce aka kama ta a unguwar FESTAC dake Lagos.

Loretta ta amsa laifin sayar da jaririn kan kuɗi miliyan ₦2,350,000.

A ƙarshe sanarwar ta ce an kama waɗanda suka saya jaririn ne daga wajenta lokacin da suke gudanar da bikin raɗin sunansa.

More from this stream

Recomended