
Hatsarin wata babbar mota ya hallaka akalla mutane hudu a Dutse-Baupma dake kallon gidan man AYM Shafa akan titin Dutse-Bwari a yankin Bwari dake birnin tarayya Abuja.
Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 12 na rana sakamakon shanyewar birkin motar daukar ya shi ya kuma rutsa da wasu motoci da suka hada da Toyota Highlander, Bakar Hilux babur mai kafa uku da kuma wata motar yan sanda.
Abdul Mohammed wanda ya sheda faruwar hatsarin ya ce birki ne ya daukewa tifar a dai dai mahadar Usman Dam akan titin Dutse-Bwari inda ta je ta ci karo da motocin kuma kusan dukkanin mutanen da suke ciki suka rasa rayukan su.
Direban babbar motar, na daga cikin mutanen da suka mutu.