Musulman Rohingya na tsaka-mai-wuya – BBC News Hausa

0

‘Yan Rohingya sun shekara biyu da gudun hijra

Dubban musulmi ‘yan kabilar Rohingya ne suka yi wani tattaki a cikin sansanonin ‘yan gudun hijra da ke Bangladesh ranar Lahadi, shekaru biyu cif-cif bayan barin mahallinsu.

Kusan mutum 750,000 ne suka bar jiharsu ta Rakhine da ke kasar Myanmar a watan Agustan 2017, sakamakon yawaitar hare-hare a kan ‘yan kabilar.

A ranar Alhamis ne kasar Bangladesh ta bullo da wani shirin mayar da ‘yan gudun hijrar garunsu idan har suna son komawa, to amma ba a samu mutum ko daya ba da ya ce yana son komawa Myanmar ba.

Suna kira ga kasar ta Mynamar da ta fara ba su takardun shaidar ‘yan kasa kafin su amince su koma kasar.

‘Yan kabiular Rohingya dai musulmai ne ‘yan tsiraru a kasar Myanmar inda mafi yawansu ke zaune a jihar Rakhine, kuma suna da yarensu da al’adunsu daban da na sauran ‘yan kasar.

To sai dai duk da kasancewarsu sun kwashe shekaru masu yawa a Myanmar, har yanzu ba a daukar su a matsayin ‘yan kasa ballatana a shigar da su kidaya.

Myanmar dai na daukar ‘yan Rohingya da masu cirani daga kasar Bangladesh.

A ranar 25 ga watan Agustar 2017, mayakan sa-kai na Rohingya suka kai wa gomman ofisoshin ‘yan sanda hari inda suka kashe jami’ai da dama.

Gwamnatin Myanmar ta mayar da martani ta hanyar kone wasu kauyuka kurmus da kama jama’a da yi wa fafaren hula fyade har ma da kisa.

Masu bincike na majalisar dinkin duniya sun gano har da zauna-gari-banza ‘yan kabilar Buddha a cikin wadanda suka kai wa ‘yan Rohingya din hari.

  • Musulman Rohingya na fuskantar wariya – Amnesty
  • Bangladesh ‘za ta mayar da Musulmin Rohingya 300’ Myanmar

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana al’amarin da “Babban misalin yadda ake yi wa al’umma kisan kiyashi;

Su kuwa ‘yan kabilar ta Rohingya na ayyana wannan rana da ranar “tunawa da kisan kiyashi.”

Sojojin Myanmar sun ce suna daukar matakan dakile ta’addanci ne kuma aikin nasu bai shafi fararen hula ba.

Wani binciken cikin gida da aka gudanar 2017 ya wanke sojojin daga zargin da ake yi musu na kisan gilla.

Yanzu ina makomar ‘yan Rohingya?

Kimanin masu gudun hijra miliyan daya ne dai ke zaune a Bangladesh, mafi yawancinsu na zaune ne a manyan sansanoni masu gudun hijrar, inda sansani mafi girma shi ne mai dauke da mutum fiye da rabin miliyan, al’amarin da ke ci wa Bangladesh tuwo a kwarya.

A farkon wannan shekarar, Bangladesh ta ce ba za ta kuma sake karbar karin masu hijrar ba, bayan da yarjejeniya tsakanin kasar da Myanmar ta ci tura a Janairun 2018 da manufar mayar da ‘yan Rohingya gida.

A lokacin dai Myanmar din ta amince ta bai wa ‘yan Rohingya ‘yancin walwala bisa sharadin mallakar katin shaidar dan kasa, to amma ‘yan Rohingya sun ce ba su amince ba domin hakan wani wata yaudara ce ta tilasta musu su amince cewa su ‘yan cirani ne a kasar.

A yanzu haka akwai ‘yan Rohingya da ba su samu sun tsere ba kimanin dubu 500 da ke zaune a jihar Rakhine. Suna zargin gwamnati da tursasa musu.

Shirin mayar da ‘yan Rohingya gida ranar Alhamis din da ta gabata ya kunshi iyalai 300 da aka kai musu bas-bas domin kai su kasarsu.

Hukumar Kula da ‘Yan gudun Hijra ta Majalisar Dinkin Duniya wadda ta tattauna da iyalan domin jin ko suna son komawa garuruwan nasu, ta ce “Har kawo yanzu babu wani daga cikinsu da ya nuna sha’awar komawa.”

Bangladesh ta fara gajiya da ‘yan Rohingya, Daga wakilin BBC a Dhaka, Akbar Hossain

Batun ‘yan gudun hijrar Rohingya na janyo wa firaiministar kasar Bangladesh, Sheikh Hasina, fuskantar matsin lamba kasancewar mutanen kasar sun gaji da ‘yan Rohingya.

Masana da dama a Bangladesh sun amannar cewa China na da hannu wajen matsawa Mynamar lamba da ka da ta kuskura ta bai wa ‘yan kabilar ta Rohingya fuskar komawa kasar.

Wani babban dalilin shi ne tabarbarewar doka da oda a sansanonin ‘yan gudun hijrar, inda a lokuta da dama a kan samu yanayin da wasu daga cikin ‘yan Rohingya ke rike makamai kuma suna kara karfi.

Da dama dai na fargabar yaduwar tsananin kaifin addini a sansanonin sakamakon kangin talauci da masu hijrar ke fama da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here