Muna kokarin sasanta Ganduje da Sarkin Kano, inji Shekarau

Tsohon gwamnan Kano kuma Sanatan Kano ta Tsakiya a yanzu Mallam Ibrahim Shekarau, ya ce yana aiki ta karkashin kasa domin ganin an samu masalaha tsakanin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Yayin wata ziyara da ya kai ofishinmu na Landan, tsohon gwamnan ya ce a matsayinsa na daya daga cikin ‘yan majalisar sarki kuma jigo a gwamnatin Kano ba abu ne mai yiwuwa ya fito karara yana tsokaci a kan al’amarin ba.

Domin haka za su ci gaba da aiki ta karkashin kasa don cimma masalaha a tsakanin shugabannin biyu.

Shekarau yana wannan magana ne a karon farko tun bayan fara takun sakar yayin da ya cika shekarara 10 da samun sararutar Sardaunan Kano, wadda marigayi Sarki Ado Bayero ya nada shi.

”Ita masalaha, kamar ciwo ne, rana daya sai ciwo ya shige ka amma sai ka shekara, shekaru ma kana shan magani ba ka warke ba” inji Shekarau.

Ya kuma bayyana cewa yana sane da kima da martabar masarauta, kana kuma ya san kima da martabar gwamnatin Kano don haka za su ci gaba da yunkurin ganin an sasanta.

Duk da cewa an dan samu sassauci kan bayyanar sabani tsakanin sarki da gwamna, an ci gaba da zaman ‘yan marina tsakaninsu, inda kowa yake harkarsa ba tare da shigar da dayan ba.

A watan Mayun bana ne gwamnatin Kano ta kirkiri sababbin masarautu hudu a Kano, abin da wasu suke ganin an yi ne domin kassara karfi da tasirin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Gwamnati ta ce an kirkiro sababbin masarautun ne domin tabbatar da ci gaba.

More News

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...