Muhawara A Kan Kirkiro Sabbin Masarautu A Jihar Kano

A yayin da ake ta cece kuce kan raba masarautar Kano zuwa gida biyar, Farfesa Samuel Zalanaga wani Dan Najeriya mazaunin kasar Amurka, kwararre a fannin ilimin rayuwar dan adam da zamantakewa, ya yi tsokaci akan matakin da majalissar Jihar Kano ta dauka.

A cikin hirarsu da Grace Alheri Abdu, Farfesa Zalangal ya bayyana cewa, abunda yafi muhimamacin a Arewacin Najeriya shine, hanyoyin da shuwagabanni zasu bi domin Inganta rayuwar talakawa da duk al’ummar kasar. Ya ce, ya kamata shuwagabbanni kamar su gwamnoni da sarakuna su hada kai suyi aiki tare domin su kawo ci gaban da al’ummar arewacin Najeriya zasu amafana, ba wai abinda zai kawo rikici da raba kawunan jama’a ba.

Idon muka duba tarihin masarautar Kano an kafata ne tun lokacin Jihadi a shekarar alif dari tara da hudu, 1804. Bai kamata ace a yanzu anzo an canja wannan tsarin ba.

Ya kara da bada Misali da Kasar Malaysia wadda ta kasance cikin kasashe masu tasowa amma ta samu ci gaba sosai saboda hadin kan al’ummar kasar.

Daga karshe ya yi ga Al’ummar Najeriya da su hada kansu domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali domin sune babban ginshikin tattalin arzikin kasa.

More News

An ƙona sakatariyar ƙananan hukumomi 2 a jihar Rivers

Wasu da ake kyautata zaton ɓatagari ne sun ƙona wani sashe na sakatariyar ƙananan hukumomin Eleme da Ikwerre dake jihar Rivers. Ƙona ginin na zuwa...

Ƴanbindiga sun hallaka wani shugaban APC a Kebbi

Wasu ‘yan bindiga sun harbe Bako Bala, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Suru a jihar Kebbi, a yayin wani yunkurin yin garkuwa da...

Kotu ta hana VIO kamawa, tsare motoci ko cin tarar direbobi a kan hanya

Justis Evelyn Maha ta Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da umarni da ya hana Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa, wanda aka...

Sojojin Najeriya sun hallaka masu haramtacciyar harƙar man fetur

Dakarun runduna ta 6 ta sojojin Najeriya sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin barayin man fetur ne, tare da cafke wasu 18...