Monaco ta bayyana Moreno a matsayin kocinta

Moreno

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kungiyar Monaco ta sanar da daukar Roberto Moreno a matsayin sabon kocinta, domin maye gurbin Leonardo Jardim.

Jardim ya lashe kofin Ligue 1 da Monaco tare da Kylian Mbappe da Bernardo Silva a kakar 2016/17.

Kafin Kirsimetin bana, Jardin ya doke Lille da ci 5-1, amma hakan bai hana mahukuntan kungiyar su sallame shi ba, tun kan ‘yan wasa su koma atisaye ranar 29 ga watan Disamba.

Tun farko Monaco ta yi sha’awar daukar tsohon kocin Valencia, Marcelino, amma ta amince da bai wa Moreno aikin.

Moreno tsohon kocin tawagar Spaniya ya saka hannu kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar tamaula ta 2022.

AS Monaco tana mataki na bakwai a kan teburin Ligue 1, bayan buga wasa 18, ta yi nasara a takwas da canjaras hudu aka doke ta a fafatawa shida.

More News

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...