Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, bisa zargin yi wa Fulani barazana a wani faifan bidiyo.
A ranar Litinin, dan a-waren ya shaida wa magoya bayansa cewa kada su jira gwamnatin kasar kafin ta dauki matakin yaki da Fulani makiyaya, wadanda ya yi zargin suna hana manoman yankin shiga gonakinsu a yankin Kudu maso Yamma.
“Wannan yanki ne namu. Mu kubutar da kanmu daga hannun Fulani. Ya kamata mu sanya tsaro a duk ƙasar Yarbawa. Ba mu buƙatar jiran kowa, har da gwamnati. Idan da gaske muke yi , bai kamata mu jira gwamnati ba, in ba haka ba Fulani za su ƙwace filayenmu gaba daya. Ya kamata mu kasance da haɗin kai. Wadanne gonaki ne muke da su kuma a kasar Yarbawa? Za mu iya zuwa gona a yanzu?”, Mista Igboho ya ce.
Da yake mayar da martani ga sanarwar, shugaban kungiyar ta MACBAN na kasa, Baba Othman Ngelzarma, ya yi kira da a kama Mista Igboho tare da gurfanar da shi a gaban kuliya saboda ya yi “kalamai na cin amanar ƙasa.”