‘Ministan Kudi bai ce a biya N105 a matsayin mafi ƙarancin albashi’

Fadar shugaban kasa ta bayyana a matsayin karya ne labarin da ake yadawa cewa ministan kudi kuma ministan tattalin arziki Wale Edun ya gabatar da N105,000 a sabon tsarin mafi karancin albashi.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a shafin sa na X ranar Alhamis.

Mai taimaka wa shugaban kasa ya rubuta cewa, “Mai girma Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, bai bayar da shawarar biyan mafi karancin albashi na N105,000 ba.

More from this stream

Recomended