Minista Sadiya Umar Farouq Ta Auri Iya Mashal Sadique?

VOA Hausa

Kafafen yada labarai a Najeriya na ta yamadidin cewa Babban Hafsan Hafsoshin saman kasar, Air Marshall Sadique Abubakar ya angwance da Ministar Harkokin jinkai Sadiya Umar Farouq.

Jaridar Daily Trust ta ce tabbatattun bayanai na nuna cewa Babban Hafsan lalle ya auri Ministar ranar jummu’a 18/09/20, inda aka daura auren a wani masallacin dake unguwar manya wato, Maitama dake Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.

Kodayake Babban Hafsan da kuma Ministar duka ba wanda ya ce kome akan batun.

Babban Hafsan sojojin saman Najeriya Air Marshall Sadique Abubakar
Babban Hafsan sojojin saman Najeriya Air Marshall Sadique Abubakar

Bnciken da wakilinmu yayi a hedikwatar sojojin Najeriya da ma makusantan Ministar dukkanninsu sun ce basu san kome akan wannan labarin ba.

Wakilinmu ya kuma tuntubi wani babban abokin Babban Hafsan wanda ya ce shi ma ya tambayi abokin nasa amma ya ce mai labatin shiririta ne.

Mai sharhi kan al’amuran zamantakewa, Mohammed I. Usman ya ce kodayake babu wani abin mamaki in har wannan aure ya tabbata, to amma ganin Habban Hafsan ya yi watsi da maganar lokacin da abokansa suka tuntubeshi to ai karshen zance kenan.

Komadai menene gaskiyar wannam batu, lokaci ka iya bayyanawa.

More News

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...