Me ya sa mutane ke kashe kansu a kwanan nan a arewacin Najeriya?

Suicide

A baya-bayan nan, ana samun ƙaruwar matasa masu kashe kansu bisa wani dalili na ɓacin rai ko kuma saboda wata matsala ta ƙwaƙwalwa.

Sau da yawa a kan yi mamakin abin da zai sa mutum ya ɗauki rayuwarsa da kansa, musamman a lokutan da a zahiri ba a san yana fama da wata lalura ta taɓin hankali ko tsananin damuwa ba.

Ƙwararru sun ce abubuwa da dama ne ke taruwa a lokaci guda har su yi sanadiyyar mutum ya kashe kansa.

Ga wasu daga cikin abubuwan da ke iya janyowa mutum ya kashe kansa:

Cutukan da suka shafi ƙwaƙwalwa

Mutane da yawa da ke kashe kansu na fama da cutukan ƙwaƙwalwa kamar cutar tsananin damuwa ko hauka da ba a sani ba.

Cutar tsananin damuwa kan daÉ—e a jikin mutum ba a sani ba kuma tana jawo wa mai fama da ita tsananin takaici da cire tsammani da rayuwa.

Don haka sai su shiga halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi su ga ba su da mafita, sai su ɗauki ransu.

Akwai abubuwa da dama da ke haifar da cutar tsananin damuwa kamar sauye-sauye na rayuwa, rashin aikin yi, rashin

Haka ma cutar taɓin hankali wanda ke janyo wa mai fama da ita gane-gane da jiye-jiye muryoyi.

Cutar taɓin hankali na hauka kan janyo mutum ya riƙa tunanin abubuwan da ba su ba ne, misali ya ga kamar wani na shirin cutar da shi ko kashe shi.

Wannan kan sauya wa mutum tunani har ya kai ga ya yanke shawarar kashe kansa ya huta.

Shan miyagun ƙwayoyi da barasa na sauya tunanin mutum har ya ji gara ya kashe kansa.

Haka kuma, masu shaye-shaye kan yi gaggawar É—aukar mataki a lokacin da suke cikin maye fiye da a lokacin da ba a maye suke ba.

Sannan shaye-shaye ya fi yawa a mutane masu fama da cutar tsananin damuwa da sauran cutukan ƙwaƙwalwa, don haka idan suka haɗu suna iya sa mutum ya shiga halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi.

A lokacin da mai shaye-shaye ya fara wato kafin abin da ya ke sha ya zama masa jaraba, ya kan yi tunanin zai iya daina sha ko rage sha.

Amma a hankali, sai jikinsa ya ƙara buƙatar abin da yake sha, wato ƙwaya ko giya. Har sai ta kai ba ya iya rayuwa sai ya sha.

Wannan kan haifar da matsaloli ga mai fama da wannan lalura har ya fidda tsammani da rayuwa ko kuma ya samu taɓin hankali har ya kashe kansa.

Rashin bacci

Abubuwa da dama na janyo rashin bacci kamar wani ciwo ko É—aukewar numfashi a lokacin bacci ko fitsarin kwance ko yawan tashi fitsari da dai sauransu.

Haka kuma, wani lokaci cutar tsananin damuwa ko cutar fargaba ta anxiety na janyo rashin bacci, haka ma rashin baccin na janyo wadannan cutukan.

Rashin bacci kwata-kwata ko rashin isasshen bacci na yin mummunan tasiri kan lafiyar ƙwaƙwalwa ta hanyar tado duk wata damuwa ko fargaba da mutum ke fuskanta.

Idan suka yi tsanani kuma ba a nemi taimakon likita ba yadda ya kamata, su kan ja mutum ya fara tunanin katse rayuwarsa.

Jaridar Psychology Today ta ce bincike ya nuna rashin isasshen bacci na janyowa mutum ya fara tunanin kashe kansa.

Masana kimiyya sun ce alamomin da ake ji a yanayi na rashin bacci ba sa da alaƙa da alamomin cutar tsananin damuwa, amma wannan ba ya nufin cewa cutar tsananin damuwa ba ta sa mutum ya kashe kansa.

Likitoci na ba da shawarar samun bacci akalla awa bakwai zuwa takwas ga babban mutum. Da zarar an fara samun matsalar bacci a je asibiti don neman taimakon likita.

Alamomin da ake gani a mutanen da ke shirin kashe kansu

  • Yawan magana kan kisan kai ko mutuwa – misali cewa “gara in mutu in huta” ko “Dama Allah Ya É—auki raina” da dai sauransu.
  • Nemo hanyoyin kashe kai kamar siyan bindiga ko guba
  • Janye jiki daga mutane da son zaman kaÉ—aici
  • Yawan fushi da kunci da cire tsammani da rayuwa
  • Yawan shan miyagun Æ™wayoyi da barasa
  • Daina cin abinci da kula da lafiyar jiki
  • Gudanar da abubuwan da ka iya hallaka mutum kamar yin tukin mota ko babur na ganganci ko amfani da Æ™wayoyin da ka iya cutar da mutum
  • Barin wasiyya babu gaira babu dalili
  • Yin bankwana da mutane ba don mutum zai yi wani balaguro ba kuma kamar ba za a sake haÉ—uwa da su ba
  • Sauyi a halayya ko kuma shiga fargaba mai tsanani

Ƙwararru na cewa ba a cika ganin alamomi a tattare da masu son kashe kansu ba, wani lokaci kuma alamomin sun danaganta daga mutum zuwa mutum.

Wasu kan bayyana cewa suna son su kashe kansu don su ‘huta’ yayin da wasu kuwa ba sa bayyanawa don haka ba za a gane ba har sai lokaci ya kure.

Haka kuma, ana ganin alamomin a yara da manya da tsoffi duka.

Abin da ya fi dacewa shi ne idan kuka ji wasu daga cikin alamomin ko kuka ga wani da waÉ—annan alamomin, a gaggauta zuwa asibiti.

Cutar tsananin damuwa da ta fargaba duk suna da magani kuma ana ba da taimako a asibiti.

More News

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...