Kasashen duniya sun fara nuna damuwa kan daukewar internet a kasar Iran, a dai-dai lokacin da aka shiga kwanaki hudu da daukewar.
Wannan ya biyo bayan zanga-zangar da ‘yan kasar ke yi kan Karin farshin man fetur da kasha 50, wanda gwamnatin shugaba Hassan Rouhani ta yyana.
A daren Asabar ne internet din ta fara fuskantar tangarda, kafin wayewar garin Lahadi ta dauke baki daya.
Iraniyawa mazauna kasashen ketare sun yi ta wallafwa a shafukan sada zumunta cewa daukewar internet ta raba su da ‘yan uwa da abokan arziki da ke gida lamarin da ya sanya ba su san a halin da suke ciki ba.
- An kashe masu zanga-zanga 106 a Iran – Kungiyar Amnesty
- Iran ta ‘samu rijiya mai gangar danyen mai biliyan 53’
Abin ya matukar tayar da hankali a kasar mai al’umma miliyan 80 da yawancin matasa sun dogara da internet dan gudanar da rayuwar yau da kullum ciki har da karatu.
Ba kamar sauran kasashen waje ba kamar Birtaniya da suke da kamfanonin sadarwa da internet daban-daban ba, wanda da wuya su iya daukewa a lokaci guda.
Iran na da kamfanoni biyu kwarara da kuma suke karkashin gwamnati, dan haka ne abin ya yi matukar tasiri.
Wata matashiya Arash Azizah ta wallafa a shafinta na Twitter yadda lamarin ya shafe ta;
”Kamar sauran Iraniyawa, muna da dandalin Whatsapp da zuriyar gidanmu ke amfani da shi, kakarmu a duk asubahin Allah ta na tura mana sakon fatan alkhairi da kariya daga dukkan abin ki, amma wannan matsala da aka samu ta hana mu yin hakan.”