Mayakan Boko Haram 314 sun mika wuya ga sojoji a Bama

Rundunar sojan Najeriya na cigaba da samun gagarumar nasara a yakin da take da mayakan Boko Haram..

A sakamakon kakkauta farmaki da hare-hare da rundunar sojan take yanzu haka mayakan kungiyar na cigaba da ajiye makamai tare da mika wuya sojoji.

A ranar Laraba 29 ga watan Yuni mayakan kungiyar 314 ne suka mika wuya ga jam’ian sojan Najeriya a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Har ila yau rundunar sojan ta samu nasarar ceto wasu manoma 12 daga hannun yan kungiyare ta Boko Haram

More from this stream

Recomended