
Kwamanda rundunar tsaron haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai a yankin arewa maso yamma General I.S Ali ya ce mayakan Boko Haram 8 ne suka mika wuya ga rundunar a ranar Laraba.
Ali wanda ya bayyana haka lokacin da yake miƙa ragamar jagorancin rundunar ga Major General Gold Chibuisi ya ce kawo yanzu sama da yan ta’adda 100,000 ne tare da iyalinsu suka mika wuya ga rundunar a yankin arewa maso gabas.
“Jiya-jiyan nan (Laraba) 8 daga cikinsu suka zo tare da bindigoginsu.”
Ya kara da cewa rundunar a karkashin sa cikin watanni shida ta samu nasarar kai farmaki da dama ciki tare da kwato makamai a wuraren irin su Ukuba dake cikin dajin Sambisa.