Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun yankewa wasu masunta biyu hannu da suka zarge su da yin sata a karamar hukumar Marte ta jihar Borno.
Zagazola Makama masanin tsaro dake wallafa bayanai akan yankin tafkin Chadi ya ce mutane biyun na daga cikin rukunin masunta dake gudanar da sana’arsu ta kamun kifi karkashin ikon kungiyar ta ISWAP.
Bayanan da ya wallafa sun ce ƴan ta’addar ISWAP sune suke kula da ayyukan masuntar inda suke karbar haraji daga wurinsu.
Wata majiyar jami’an tsaron sirri ta ce mayaƙan na ISWAP sun kwace kunshin kifi 8 bayan da suka zargi masuntan da ƙin biyan haraji.
Ƴan ta’addan sun iya daukar kunshin kifi shida ne a cikin jirgin ruwansu abin da ya sa suka bar kunshi biyu.
Masuntan sun ɗauke ragowar kunshi biyun da aka bari abin da ya sa aka kama su da laifin sata.