Rundunar dakarun soja ta ƙasa da ƙasa wato Multi National Task Force(MNJTF) a turance shiya ta 3 dake Monguno a Najeriya ta bayar da rahoton yadda mayaƙan kungiyar Boko Haram ke cigaba da ajiye makamai suna miƙa wuya ga jami’an tsaro.
A cewar rundunar a ranar 13 ga da watan Afrilu wasu mayaƙa biyu Ahmed Isiaka da Adam Muhammad dake da shekaru 18 da 17 kowannensu suƙa miƙa wuya ga sojojin.
Matasan biyu sun fito ne daga garin Kollorom a ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.
Sun kuma miƙawa jami’an soja harsashi na musamman guda 250 mai girman 7.62mm da kuma harsashi 50 mai girma 7.62 ƙirar NATO da kuma wasu abubuwa da dama.
Idan za a iya tunawa koda a ranar 24 ga watan Maris rundunar ta MNJTF ta bayar da sanarwar cewa wasu mayaƙan Boko Haram biyu sun miƙa wuya ga rundunar.