Matsalar Almajiranci A Najeriya – laifin Wanene? | VOA Hausa

Duk da kokarin da wasu gwamnatoci da kungiyoyi ke yi game da maganar magance almajiranci a Najeriya wasu Malaman makarantun allo sun ce gwamnati ta baro shirin tun rani, game da maganar magance almajiranci a kasar.

Shugaban kungiyar malaman makarantun tsangaya a Najeriya reshen jahar Kaduna, Alaramma gwani Suleiman Idris Mai-zube, ya ce babu wani shiri kan Almajirai da zai yi nasara ba tare da shawarar malaman makarantun allo ba.

Kungiyar malam tsangaya ta fitar da tsarin inganta karatun allo da saka karatun zamani da kuma koya sana’o’i, amma gwamnati ba ta kula da tsarin ba, a cewar Alaramma Mai-zube.

Dr. Salisu Bala na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya ce an gaza wajen inganta tsarin karatun allo a Najeriya, inda ya nuna yadda wasu ke neman kudi da maganar Almajiranci a kasar.

Sai dai Hajiya Binta Kasimu wadda ke jagorancin kungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki da bankin duniya ta ce kungiyoyi ne kawai mafita kan almajiranci a Najeriya.

Hajiya Binta ta ce tuni bankin duniya ya gane hanyar amfani da kungiyoyi masu zaman kansu maimakon gwamnatocin Najeriya a matsayin mafita kan maganar barace-barace a kasar.

More News

Buhari ya rantsar da sabon Alkalin Alkalai

Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya rantsar da mai shari'a, Olukayode Ariwoola a matsayin, babban Alkalin Alkalai na Najeriya. Hakan na zuwa ne biyo bayan murabus...

‘Kyale kowa ya mallaki makami a Zamfara na da haɗari’

Masana a harkar tsaro sun bayyana cewa matakin da gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta dauka na kyale farar-hula su mallaki bindiga yana...

Hotunan Daurin Auren Dan Gwamnan Nasarawa

Manyan baki da dama ne ciki har da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo suka halarci daurin auren dangidan gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da...

Hotunan Daurin Auren Dan Gwamnan Nasarawa

Manyan baki da dama ne ciki har da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo suka halarci daurin auren dangidan gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da...