
Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta ziyarci tsohon shugaban kasa, Muhammad Buhari a gidansa dake Daura.
A yayin ziyarar uwargidan shugaban kasar na tare da, Nana Kashim Shettima matar mataimakin shugaban kasa, ta ce ta kai ziyara ne domin ta gaishe da Buhari da kuma yi masa godiya kan goyon bayan da yake basu irin na mahaifi.
A wata sanarwa mai magana da yawunta, Busola Kukoyi ta ce Remi ta yi addu’ar tsawon rai da kuma lafiya ga Buhari.
Ana sa jawabin Buhari ya nuna godiyarsa bisa ziyarar inda ya ce za ziyarar za ta zama abin tunawa.