
Matar shahararren dan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Barau Mangal ta rasu.
Hajiya Aisha Dahiru Mangal ta rasu a wani asibiti dake Abuja da maraicen ranar Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya.
An gudanar da jana’izar marigayiyar ranar Lahadi da misalin karfe 11:00 na safe a Katsina.
Marigayiyar ta rasu ta bar mijinta yaya da kuma jikoki.