Matakan da suka kamata Buhari ya ɗauka domin fitar da Najeriya daga matsalar tattalin arziki

Naira

Masana tattalin arziki a Najeriya sun matakan da suke gani sun kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya ɗauka domin ceto ƙasar daga koma-bayan tattalin arzikin da ta faɗa a cikin irin sa mafi girma cikin fiye da shekara 30.

A ƙarshen makon jiya ne hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta fitar da wata sanarwa da ta nuna cewa Najeirya ta fada matsin tattalin arziƙi karo na biyu cikin shekara biyar.

Farfesa Mustapha Muktar, malami ne a sashen nazarin tattalin arziki na jami’ar Bayero da ke Kano, ya ce idan aka samu irin wannan matsala akwai matakai da dama da ake ɗauka wajen ganin an rage kaifin wannan matsala ko kuma an fita daga cikinta baki ɗaya.

“Ana iya fara komawa kasafin kuɗin ƙasa da aka yi a duba shi cikin nutsuwa, sai a rage duk wani abu da ake zaton muhimmancinsa bai kai ya kawo ba a halin da ƙasar ke ciki, domin a yi komai daidai ruwa daidai tsaki,” in ji shi.

“Za kuma a iya komawa ga duka ɓangarorin tattalain arziƙin ƙasar a duba wanne ɓangare ne ya janyo koma-bayan domin a magance shi. Misali, ɓangaren masana’antu ne ko kuma ɓangaren ayyukan yau da kullum.

“Na uku, hukumomi su yi ƙoƙari su samar da ayyukan yi da kuma samar da bashi ga ƙanana da kuma manyan masana’antu, ko kuma su sassuta harajin da ake karɓa daga hannunsu,” a cewar Farfesa Mustapha.

A nasa ɓangaren, Farfesa Nazifi Darma, malamin tattalin arziki a jami’ar Abuja, yana ganin da a ce gwamnatoci a dukkan matakai – daga Tarayya da jihohi da kuma ƙananan hukumomi – za su ƙarfafa wa al’umma gwiwa wajen dogaro da kansu da an samu mafita.

“Saboda haka duk ƙoƙarin ɗan kasuwa idan gwamnati ba ta samar da tsare-tsare masu kyau da za su taimaka wa kasuwancinsa ba to babu in da za a je,” in ji Farfesa Darma.

Ya ƙara da cewa Najeriya na buƙatar tsarin tattalin arziƙi na dogon zango domin kuwa zai taimaka wajen dakushe matsalolin da za su riƙa tasowa a kusa a faɗn kasar baki ɗaya.

Mecece matsalar komabayan tattalin arziki?

Duka waɗannan farfesoshi sun amince cewa matsalar koma-bayan tattalin arziki na faruwa ne lokacin da alƙaluma na mizanin auna tattalin arziƙi (GDP) da ake amfani da su duk bayan wata uku suka nuna an samu koma-bayan arziki a watanni shidan na cikin shekara.

Ba wani abu ba ne ɓoyayye a duniya ko wacce ƙasa na fuskantar bunƙasa ko kuma koma bayan tattalin arziki lokaci zuwa lokaci. Amma wannan ya danganta da matsalolin da ƙasa ke fuskanta da ke sanya ma’aunan tattalin arziki bunƙasa ko kuma akasin haka.

Da yawa mutane na ganin GDP a matsayin kuɗin da ƙasa ke samu na cikin gida kawai, amma ma’anarsa ta wuce haka saboda yana auna duka hada-hadar da ake yi a ƙasa, kama daga abin da gwamnati take kashewa da abin da take tsammanin samu, in ji Farfesa Darma.

Alƙaluman ma’aunin tattalin arziki da ake kira GDP suna da faɗi, amma sun hada:

  • Bangaren Noma
  • Masana’antu
  • Gine-gine
  • Sadarwa
  • Ɓangaren Abinci
  • Ayyukan yau da kullum
  • Kuɗaɗan da ake aikowa ƙasar daga kasashen wajen
  • Kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa da wanda take tsammanin shigowarsu

Bugu da ƙari da sabon tsarin haɗewar duniya wuri guda (Globalization) da kuma yadda ciniki ke ƙara buƙasa tsakanin ƙasashen duniya, “ya sanya ana ƙirga hada-hada tsakanin kasuwanni cikin wannan ma’auni,” in ji Farfesa Nazifi.

Me ke sa wa a faɗa wannan matsala?

Abubuwan da ke sa wa a faɗa irin matsalar tattalin arziƙi na da yawa amma domin masu karantawa su gane za mu raba su kashi biyu, in ji Dakta Shamsudden Muhammad na jami’ar Bayero a Najeriya.

Buƙatun ‘yan ƙasa da gwamnati da masana’antu: Lokacin da ya kasance ‘yan ƙasa ba sa iya sayen abin da suke so komai ya yi tsada ga ƙarancin kuɗaɗe a hannun mutane, wannan dalilin zai iya sanya tattalin arziki ya yi baya ƙasa ta shiga abin da ake kira matsin tattalin arziki ko recession a turance.

Durƙushewar ɓangaren waɗanda suke samar da kayayyaki: Idan ya kasance masana’antu ba sa iya samar da kayayyakin da suke sarrafawa saboda dalilai kamar na su yaƙi ko kuma tsauraran dokoki na gwamnati na haraji, ko kuma ita gwamnati a nata ɓangaren ba ta iya samar da man fetur da take haƙowa ko kuma buƙatarsa ta yi baya a kasuwar duniya, to su ma za su iya kai wa ga faɗawa matsalar tattalin arziƙi.

Bayanan hoto,
Matsalar cutar Covid-19 da ta ja aka kukkule harkokin kasuwanci, kamar su ƙere-ƙere da harkokin sufuri na daga cikin abubuwan da suka janyo wannan koma baya.

Dakta Shamsudden ya ce amma a Najeriya “matsalar cutar Covid-19 da ta ja aka kukkulle harkokin kasuwanci, kamar su ƙere-ƙere da harkokin sufuri na daga cikin abubuwan da suka janyo wannan koma-baya.

“Sai kuma dokoki da gwamnati take yi da kwata-kwata ba sa taimakawa masana’antu, kamar ƙarin kuɗin haraji da ƙarin kuɗin makamashi da rashin wutar lantarki da kuma faduwar darajar naira su ma sun ba da gudunmawa”.

“Kan talaka matsalar ke ƙarewa”

Farfesa Nazifi Darka ya ce kai-tsaye wannan matsala kan talaka take ƙarewa saboda idan an tashi korar aiki a masana’antu talaka ake kora.

Idan abubuwan rayuwa sun yi tsada talaka ne ke gaza saya domin haka yana ji a jikinsa.

Ko ƙarin ƙudin makaranta aka yi kan shi ƙarin ke ƙarewa, idan yunwa ce ake fama da ita ba za ka taɓa jin wani shugaba ko mai kuɗi na yi maka kukanta ba, in ji shi.

More News

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...