Manyan lauyoyi za su dunguma don kare Onnoghen a gaban Kotu

Justice Walter Onnoghen
Hakkin mallakar hoto
National Judicial Council

Wasu shaharrrun lauyoyi a Najeriya sun tabbatar da cewa za su sadaukar da ayyukansu domin bayyana a gaban kotu da nufin ba da kariya wa Alkalin Alkalan kasar, mai shari’a Walter Onnoghen a kotun da’ar ma’aikata.

A ranar litinin ne kotun da’ar ma’aikata ta ce Alkalin alkalan zai gurfana gabanta kan zargin kin bayyana dukiyar da ya mallaka.

Batun dai ya janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya musamman lokacin da kasar ke tunkarar babban zabe. Kamfanin dillacin labaru na Najeriya NAN ya ruwaito cewa cibiyar da ke bincike kan rashawa ARDI ita ce ta fara shigar da koken kan Alkalin Alkalan.

Bisa tsarin doka dole ne manyan ma’aikata da jami’an gwamnati su bayyana dukiyar da suka mallaka kafin karbar mukami da kuma bayan sun sauka a wani mataki na yaki da rashawa.

Mista Agbakoba ya shaida wa sashen turancin broka na BBC cewa hukumar NJC da ke sa ido kan al’amurran shari’a a Najeriya ce ya kamata ta dauki matakin.

Ya ce NJC da dukkanin alkalan Najeriya ke karkashinta ya kamata ta dauki matakin a kan Alkalin Alkalan.

Ya kara da cewa mai shari’a Onnoghen yana da rigar kariya kuma za a iya wanke shi.

Laifuka shida ake tuhumarsa, dukkaninsu da suka shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka.

Hakkin mallakar hoto
OAL.LAW
Image caption

Tsohon shugaban kungiyar lauyoyi na Najeriya Olisa Agbakoba

Tsohon shugaban kungiyar lauyoyin ya ce yana cikin wadanda za su kare Alkalin alkalan.

Ya kuma ce hanyoyi biyu kawai ake bi domin iya tsige Alkalin Alkalai da kundin tsarin mulki ya tanadar. Shi ne idan an gabatar da shi a ‘yan majalisar dattawa kuma kashi biyu bisa uku sun jefa kuri’ar tsige shi.

Ko kuma Hukumar da ke kula da shari’a NJC ta tsige shi da kanta.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...