Manyan abubuwan da suka faru a wannan makon | BBC Hausa

Image caption

Gawar sojojin da aka kashe a Nijar

Jana’izar sojojin da aka kashe 73

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamadou Issoufou, ne ya jagoranci jana’izar sojoji 71 da kungiyar IS ta kashe yayin harin da ta kai kan wani sansanin sojin kasar a yankin Tillabery ranar Talata.

Tuni dai shugaba Issoufou ya sanar da fasa gudanar da bukukuwan cikar kasar shekara 59 da samun ‘yancin kai da za a yi ranar Laraba mai zuwa a birnin Niamey.

Gabani nan Mahamadou Issoufou ya sanar da katse ziyarar aikin da yake yi a Masar lokacin da ibtila’in ya faru, domin nuna alhinin rasuwar dakarun nasa.

Image caption

Jariran da ke da kwayar cutar HIV na da yawa a Najeriya

Najeriya ce da daya wajen yawan kananan yara masu cutar HIV

Karamin ministan lafiyar Najeriya Sanata Adeleke Mamora, ya ce kasar ce tafi kowacce kasa yawan jariran da ke dauke da kwayar cutar HIV mai karya garkuwar jiki.

Ya ce hakan ne ya sa gwamnati za ta ci gaba da gudanar da ayyukan samar da garkuwa daga kamuwa da kwayar cutar mai karya garkuwar jiki a fadin kasa.

Sanata Mamora kamar yadda jaridar Punch ta rawaito, ya ce gwamnati za ta zuba makudan kudade da ma’aikata da kayan aiki wajen ganin an dakile kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki zuwa 2030.

Image caption

Shugaban hukumar Kwastam Hamid Ali

Kwastam sun harbi dalibi a Kano

Rahotanni na cewa jami’an hukumar kwastam a Najeirya sun harbi wani matashi dalibi a birnin Kano wanda dan asalin jihar Yobe ne.

Dalibin ya ce jami’an sun bude wuta a kan motarsa ne bayan ya taka burkin gaggawa sakamakon ankarar da ya yi da shingen da jami’an suka kafa a kan hanyarsa ta shiga birnin Kano daga jihar Yobe.

Ya ce ma’aikatan sun yi zargin mai fasakauri ne, amma bayan da suka lura cewa ba haka ba ne sai suka ranta a na kare.

Image caption

Matar shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari

Aisha Buhari ta caccaki Garba Shehu

Mai dakin shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, Aisha ta wallafa wani rubutu da yake ta karakaina a shafukan sada zumunta, inda da kanta ta caccaki mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu.

A cikin rubutun da aka wallafa mai taken “Garba Shehu na wuce gona da iri”, mai dakin shugaba Buharin ta nuna yadda mai magana da yawun mijin nata ke ‘yi wa iyalan shugaban zagon kasa’.

Aisha Buhari ta ce “Garba Shehu na daya daga cikin masu kware wa Buhari baya kasancewar yaron wasu ne.”

Image caption

Magoya bayan Ibrahim El Zakzaky

IMN ta nemi a saki El-zakzaky

Kungiyar ‘yan Shi’a karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Elzakzaky, IMN, ta yi kira ga gwamnatin Shugaba Buhari da ta saki jagoran nata da ya kwashe shekaru hudu cif-cif yana hannun hukuma tun bayan rikicin da ‘yan kungiyar suka yi da sojoji a Zaria a 2015.

A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar ta IMN, Ibrahim Musa ya fitar, kungiyar ta ce “Yayin da muke bikin zagayowar ranar kisan kiyashin Zaria da mutuwar mambobin IMN, muna kira da a gaggauta sakin Sheikh tare da duk sauran jama’ar da ke tsare ba tare da wani sharadi ba.”

IMN ta kuma bukaci da a hukunta dukknain sojojin da suke da hannu a ‘kisan mutum kusan 1000’ da kungiyar ta yi zargin an yi a Zaria.

Hakkin mallakar hoto
Sadau Instagram

Image caption

Rahama Sadau da mawakin nan Classic

Rahama Sadau ta karade kakafan sadarwa.

Labarin Rahama sadau yayin wani biki da ya gudana a Kaduna wanda ya ja cece-kuce a kafafen sadarwa musammam Twitter da Instagram.

Masu bibiyar shafukan sun ta tafka muhawara kan yadda tauraruwar ke gudanar da rayuwarta yayin da wasu ke kare ta.

Ita ma ba a barta a baya ba ta shiga ta kuma kare kanta a wasu daga cikin sharhin da aka yi a kanta.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sarauniyar Kyau ta duniya

Sarauniyar Kyau ta Duniya

Zozibini Tunzi wadda ‘yar kasar Afirka ta Kudu ce ta lashe gasar Miss Universe ta 2019 ne da aka yi birnin Atlanta na kasar Amurka ranar Litinin.

More News

Ƴan Boko Haram sun kashe manoma a Borno

Mayakan Boko Haram sun kashe manoma 10 tare da yin garkuwa da wasu da dama a karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno. Baya...

Rikici kan abinci ya sa wani magidanci kashe matarsa.

Yan sanda a jihar Edo sun kama wani mutum mai suna, Salami Anedu ɗan shekara 21 kan zargin kashe matarsa sakamakon saɓani sa suka...

Yau da rana za a yi jana’izar Sheikh Giro Argungu

A yau Alhamis ne za a yi jana'izar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Abubakar Giro Argungu wanda ya rasu a jiya Laraba. An sanar da...

Gwamnan Jigawa zai biya wa asalin ƴan jihar kuɗin makaranta

Gwamna Umar Namadi ya amince da biyan kudin rijistar ɗaliban Jhar Jigawa wadanda suke karatun digiri daban-daban a Jami’ar Tarayya, Dutse FUD, Jami’ar Bayero,...