Mai fashin baki kan wasan kwallon kafa, Alan Shearer ya ce bai taba ganin lalatacciyar tawagar kulob din Manchester United irin ta yanzu ba bisa la’akari da yadda kulob din Newcastle ya ci Man U daya mai ban haushi, ranar Lahadi.
Tsohon dan wasan Ingilar ya bayyana hakan ne lokacin wani sharhin bayan wasanni da aka saba yi bayan wasan.
Shearer ya ce ta tabbata Manchester United ta samu baraka a bayanta da tsakiyar har ma da gaban nata.
Manchester United dai ta kara cin karo da koma baya a wasannin Premier bana, bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Newcastle United.
- Newcastle ta kara jefa Man United cikin matsi
- Dogon Mai Takwasara ya sha kisa a hannun Dan Jere
Yanzu dai Manchester United ce ta 12 a kasan teburin Premier da maki tara bayan wasa takwas da ta yi.
Ita kuwa Newcastle United ita ce ta 15 da maki takwas da tazarar maki daya tsakaninta da ‘yan ukun karshe a teburin Premier.
Wannan ce kaka mafi muni da Manchester United ta hada maki tara a karawa takwas a gasar Premier tun bayan 1989/90.