Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Kungiyar Manchester United da Arsenal sun tashi wasa 1-1 a karashen wasan mako na bakwai a gasar cin kofin Premier da suka kara a Old Trafford ranar Litinin.
United ce ta fara cin kwallo daf da za a je hutu ta hannun Scott McTominay.
Arsenal ta farke ne ta hannun Pierre-Emerick Aubameyang da farko mataimakin alkalin wasa ya ce an yi satar gida, amma da aka duba na’ura mai taimakawa alkalin wasan tamaula yanke hukunci VAR, ta ce ba satar gida.
Da wannan sakamakon Arsenal ta hada maki 12 kenan ta koma ta hudu, ita kuwa United tana da maki tara tana ta 10 a teburi, bayan da kowacce ta buga wasa bakwai-bakwai a kakar bana.
Arsenal ba ta yi nasara a gidan United a manyan wasa 13 da ta buga ba, sannan karawa uku ta ci daga 28 da ta ziyarci Old Trafford a gasar Premier.
A kakar bara sau uku Manchester United da Arsenal suka kara a tsakaninsu, inda suka yi 2-2 a gasar Premier a Old Trafford ranar 5 ga watan Disambar 2018.
Sun kuma kara a FA Cup ranar 25 ga watan Janairu, inda Manchester United ta yi nasarar doke Arsenal da ci 3-1.
Haka kuma sun hadu a gasar Premier a gidan Arsenal wato Emirates, inda Arsenal ta doke United da ci 2-0 ranar 10 ga watan Maris, 2019.
Arsenal za ta karbi bakuncin Bournemouth a wasan mako na takwas ranar Lahadi 6 ga watan Oktoba a kuma ranar Manchester United za ta ziyarci Newcastle United.