Man City: Phil Foden zai yi jinyar da za ta kai kusan mako hudu

Phil Foden

Phil Foden ba zai fara buga wa Manchester City wasannin Premier League na bana ba, sakamakon raunin da ya yi a Euro 2020.

Foden, mai shekara 21, ba zai buga wa City kusan wasa uku ba, sune da suka hada da na Tottenham da Norwich City da kuma Arsenal.

Haka kuma da kyar ne idan dan wasan zai buga wa tawagar Ingila wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya a 2022 da za ta kara da Hungary cikin watan Satumba.

Ana sa ran Foden zai koma atisaye nan da kusan mako hudu da watakila ya fara buga Premier ranar Asabar 11 ga watan Satumba a fafatawa da City za ta yi da Leicester City.

Kocin kungiyar Etihad, Pep Guardiola ya tabbatar da cewar Kevin de Bruyne na jinya, wanda ya yi rauni a tawagar Belgium a karawa da Italiya a Euro 2020.

A kakar da ta kare City ta lashe Premier League, sannan ta kai karawar karshe a Champions League – Foden ya ce za su fuskanci kalubale mai zafi a kakar bana.

More News

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...