Mahaifina bai kanainaye gwamnatin Buhari ba – Fatima Mamman Daura | BBC Hausa

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Babana bai kanainaye gwamnatin Buhari ba – Fatima Daura

Fatima Mamman Daura, ‘yar makusancin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta ce mahaifinta bai kanainaye gwamnatin Buhari ba kamar yadda wasu ke tunani.

A hirarta da BBC, Fatima ta ce mahaifinta Mamman Daura da Shugaba Buhari sun tashi tare kuma abokansu daya don haka ne ya sa kusancinsu ya yi yawa.

Ta ce “kowa na da amini, wanda yake jin maganarsa. To aminan juna ne sosai, shi ya sa mutane ke ganin kamar ya kankane gwamnatin.”

Mamman Daura dan uwa ne na kusa ga shugaban Najeriyar – Buhari kawunsa ne – kuma duk da cewa ba shi da mukami a gwamnatin amma ana hasashen cewa yana da fada-a-ji a fadar ta shugaban kasa.

Fatima ta ce ba gaskiya ne ba zancen da ake cewa mahaifinta ya kanainaye Shugaba Buharin sai yadda ya ce ake yi, “Baba mutum ne mai kawaici, ba ya son shiga ma harkar mutane kuma bai cika yawan magana ba, kuna ma iya yin bincike akai ku gani,” a cewar Fatima.

“Na san shugaban kasa kan nemi shawararsa ammaidan ya ba da shwarar ya kan janye ne ba ya katsalandan, yana gidan yana tasbihinsa, ko mun masa maganar cewa yake mu daina damuwa ana kankare masa zunubi ne.

Ta ci gaba da cewa “ba ma jin dadin abin da ake fada a kansa amma dai mun san kasancewar sy tare ne ya sa ake masa haka albarkanci zumunci.”

Hakkin mallakar hoto
Twitter

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...