Ma’aikata a jihar Benue sun samu albashi karon farko cikin watanni 6

A karon farko cikin watanni shida ma’aikatan jihar Benue sun karbi albashi.

Wasu daga cikin ma’aikatan jihar da jaridar Daily Trust ta zanta da su sun ce sun fara ganin alert a ranar Lahadi.

Wani ma’aikaci da ya samu nasa albashin ya ce ya ji farin cikin sosai lokacin da ya ga kudin.

Da dama daga cikin ma’aikatan sun ce samun albashin zai rage musu radadin zafin rayuwa da suke ciki.

More from this stream

Recomended