Lionel Messi: Wacce kungiyar ce ke da damar sayen gwarzon dan kallon duniyar?

Messi

Bayanan hoto,
Babu mamaki idan aka ce Lionel Messi ya buga wasansa na karshe a Barcelona

Kowacce kungiya a duniya hakika za ta so amfani da wannan dama ta dauki gwarzon dan wasa irin Messi dan kasar Argentina biyo bayan rahotannin da ke cewa ya mika wa Barcelona takardar bukatarsa ta barin kungiyar.

Sai dai lamarin cike yake da sarkakiya, kuma maganar gaskiya kungiyoyin kadan ne suke da damar daukar wannan dan wasa.

Messi ya kwashe shekaru yana sha’awar kwallon Premier Ingila, ba don komai ba sai don manyan abokansa da suka shafe shekaru a gasar – Sergio Aguero da Cesc Fabregas.

Akwai tabbaci kan jita-jitar cewa dan wasan zai iya komawa Manchester City.

Na farko, saboda Pep Guardiola wanda tsohon kocinsa ne da ya taimaka wajen haskakawarsa, da kuma wasu jami’ai da Messi ya zauna da su a Barcelona – Ferran Soriano da Txiki Begiristain.

City za ta iya biyan albashin da ake zaton Messi zai nema, a bangaren kwallo Messi ya san Guardiola zai iya sauya fasalin kungiyar ta yadda zai ci gaba da kokari – akwai abun da Messi ya rasa a Barcelona na tsawon shekaru.

Chelsea da Liverpool da kuma Arsenal na da burin shiga wannan ciniki, yanayin yadda iyalan Messi za su fara rayuwa a Ingila ya zama wani kalubale, amma tuni ‘ya’yansa suka fara zuwa makarantar koyon Turancin ingilishi a wani yanki a Barcelona.

Su waye masu karfin arziki a Turai?

A wani yanki a Turai, PSG da aka cire a wasan karshe na kofin Zakarun Turai na ganin wannan damarsu ce ta daukar Messi a kaka mai zuwa – kamar City, suna da karfin kudi da za su iya daukar dan wasan.

Kuma hakan zai iya zama abin da Messi zai so saboda samun damar sake haduwa da Neymar a kungiya daya, wanda barinsa Barcelona a 2017 ya zama daya daga cikin abubuwan da suka haifar da koma baya ga dan Argentina da kuma jefa kungiyar halin da ta samu kanta ciki.

A makon da ya gabata kuma Inter Milan da aka cinye a wasan karshe na Europa ta shiga neman dan wasan.

Masu kungiyar – Suning Holdings wadanda ‘yan China ne – suna da fatan kawo karshen shekaru tara da Juventus ta kwashe tana daukar gasar Serie A kuma rahotanni na cewa shugaban kungiyar Steven Zhang ya tattauna da wakilan Messi.

Wannan fatan da ake ya kara yada jita-jitar da aka rika watsawa a ranar Talata, kuma zaton da ake yi na ko Messi zai sake fuskantar Cristiano Ronaldo zai iya zama gaskiya cikin sauki.

Wadanda suka kara nuna zawarcinsu ga dan wasan a kusa su ne Real Madrid, inda aka ce tuni sun isa sansanin da Messi yake, to amma maganar gaskiya wannan cinikin ba ma zai yiwu ba, duk kuwa irin fushin da Messi ya yi da Barca.

Komawa gida ko inda aka fara?

Akwai kuma wani zabi mai dadi ga Messi; shi ne na komawa gida Agentina ya buga wa kungiyarsa ta farko Rosario Newells.

Messi zai so ya koma domin buga kwallo a kungiyar da ya fara sanya wa riga a rayuwa kafin ya yi ritaya daga kwallo kwatakwata, ba don komai ba sai don kara samarwa kansa da yaransa uku tsaro a kasarsa.

Haka kuma, za mu iya duba maganar cewa Messi zai koma kwallo a Asia.

Ta yadda abokan kwallonsa Xavi da Andres Iniesta za su ba shi labarin zamansu a Qatar da Japan, amma bambancin shi ne; su lokacin ajiye kwallonsu ne ya yi, suka ajiye a radin kansu suka bar Nou Camp.

A bangare daya kuma, Messi ya yi amannar zai buga kwallo yadda ya kamata, kuma watakila ta zama shekarar da zai kara daukar Champions da Barcelona bayan kwashe shekaru yana dibar bakin ciki a kungiyar.

Zama a Barcelona?

Nuna zai bar Barceola ba karamin tunani mai kyau ba ne, babu wanda zai iya yanke hukunci cewa dan wasan zai zauna a kungiyar tasa ta yanzu.

Ana kallon ikirarinsa na ranar Talata a matsayin wani mataki na furta abin da ke cikin ransa na damuwa da shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu.

Ko da hakan bai yiwu ba, rikicin da Bartomeu ke yi na bangaren shari’a zai ragu, wanda yake cewa Massi ba zai bar kungiyar ba tare da an biya Yuro miliyan 700 na yarjejeniyarsa ba, kuma zai kalubalence shi a kotu na yabar Barcelona babu wadannan kudade.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...