Lionel Messi: Shin wannan ne ƙarshen rayuwar Messi a Barcelona?

Messi

Asalin hoton, Getty Images

Sanarwar da Barcelona ta fitar a yammacin Alhamis ta girgiza duniyar ƙwallon ƙafa.

Wannan na zuwa ne yayin da fitaccen É—an wasan na Argentina mai shekara 34, wanda ba shi da yarjejeniya tun 1 ga watan Yuli, ke fatan sabunta yarjejeniya domin tsawaita zamansa na shekara 21 a Barcelona.

Barcelona ta ce a ranar Alhamis ya kamata Messi ya sa hannu kan yarjejeniyar, amma aka samu cikas ga dokoki da sharuÉ—an kuÉ—i na hukumomin La Liga.

Yanzu mece ce makomar ɗan wasan da ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan duniya sau shida? Shin wannan ne ƙarshen rayuwarsa a Barcelona, ko akwai wata mafita a ƙarshe?

Me ya sa yarjejeniyar ta gagara?

A farkon wannan watan, mai sharhin ƙwallon ƙafa a Sifaniya Guillem Balague ya ruwaito cewa Messi ya amince ya ƙulla sabuwar yarjejeniya har zuwa 2026 inda ya amince a datse rabin albashinsa.

Amma kuma dole sai Barcelona ta sayar da wasu Æ´an wasanta domin ta samu kuÉ—in riÆ™e Messi – wato ta rage kuÉ—in da take kashewa ga biyan albashi da kusan yuro miliyan 200 domin cimma ka’idojin La Liga na Æ™ashe kuÉ—i – amma hakan ya gagara.

Har yanzu Antoine Griezmann da Ousmane Dembele da Philippe Coutinho – da sauransu – har yanzu suna Barcelona.

A lokacin da yake tsokaci a shirin sharhin Æ™wallon Æ™afa na BBC Radio 5, Balague ya ce: “Barca ta yi Æ™oÆ™arin samo hanyoyin da za ta iya biyan albashin Messi da alawus dinsa, kuma na tambaye su, ‘ta yaya za ku cimma haka tun da kun kasa rijistar sabbin Æ´an wasa’? amsar da suka bayar ita ce ‘kawai ka yarda da mu.’

“SaÆ™on da ya fito daga É“angaren Messi shi ne, a jira.” Laporta (shugaban Barcelona) yana da kyakkyawan fata, saÉ“anin É“angaren Messi. Kuma babu wani lokaci guda da aka nuna cewa hakan ba zai yiwu ba.

“Yanzu kuma an tabbatar da cewa babu wata hanyar da za a iya tabbatar da yiwuwar hakan. Amma ko wannan zai iya zama Æ™arshen labarin.”

Ernest Macia na Rediyo Catalunya ya shaida wa BBC cewa: “mutane da dama na mamakin yadda rayuwa za ta kasance babu Messi saboda babu wanda ya taÉ“a tunanin hakan a cikin waÉ—annan kwanaki uku.

“Mun ji wasu maganganu a Æ™ungiyar, shi kansa shugaban Barca Joan Laporta yana cewa Messi zai zauna. An tanadi yarjejeniya da za a Æ™ulla an riga an rubuta.

“A cikin sanarwar kamar Barcelona da Messi sun amince – sun fahimci juna. Maimakon haka halin matsalar kuÉ—i da Æ™ungiyar ke ci, da kuma sharuÉ—É—an La Liga… amma muhimmin batun shi ne cimma sharuÉ—É—an hukumomin La Liga.

Shin wannan wasa ne?

Tsokacin Andy West mai sharhin ƙwallon ƙafa a Sifaniya

Ba lokaci ne na aika saƙwannin yin bankwana ba, kamar yadda wasu suke gani, domin sanarwar Barca ba ya nufin Messi zai tafi, da saura.

Watakila wata dabara ce ta barazana da wasa da hankalin La Liga, wadda sharuɗɗanta suka hana Messi da Barca ƙulla sabuwar yarjejeniya da suke iƙirarin cimma.

Tushen matsalar kuÉ—in Barcelona na da alaÆ™a da ra’ayinta na shirin kafa gasar Super League na manyan Æ™ungiyoyin Æ™wallon Æ™afa na Turai inda shugaban Æ™ungiyar Joan Laporta ke ci gaba fafutika tare da takwaransa na Real Madrid Florentino Perez.

Abu mai muhimmanci shi ne sanarwar Æ™ulla yarjejeniya da La Liga ta yi da kamfanin saka jari na CVC, wanda nan take Barca ta samu kusan fan miliyan 200 – kuÉ—in da ya isa ta sake Æ™ulla yarjejeniya da Messi.

Domin samun kudin, sai ƙungiyar ta jaddada amincinta da La Liga, tare da janye matakin kafa Super League.

Laporta ya faÉ—a wa shugaban La Liga Javier Tebas cewa: “Bari mu ga shirin da sabon kamfanin abokin huldarka zai yi da La Liga ba tare da Messi ba.

Me zai kasance makomar wannan matakin… wa ya sani?

Me zai kasance yanzu makomar Messi?

Ba a daɗe ba da Messi ya ce yana son yarjejeniyarsa ta ƙunshi damar ficewa a lokacin da yake so, amma Barca ta ce dole sai an biya yuro miliyan 700.

Yanzu babu wannan sharaÉ—in.

An daɗe ana alaƙanta shi da tsohon mai horar da shi Pep Guardiola na Manchester City.

Bayanan bidiyo,
Shin Messi zai koma Man City ne?

Amma City da ta saye Jack Grealish kan fan miliyan 100 tana kuma farautar É—an wasan gaba na Tottenham Harry Kane, Balague na ganin City da wuya ta iya É—aukar Messi bisa sharuÉ—É—an dokar adadin kuÉ—in sayen Æ´an wasa.

“Bisa wannan ban yi tunanin City tana da kudin sayen Messi ba, amma mun fi ganin Paris St-Germain ta latsa.”

Babban mai sharhin Æ™wallon Æ™afa a Faransa Julien Laurens ya ce a bara PSG ta ce idan Messi yana ra’ayinta tana da kudin da za ta iya sayensa.

(BBCHausa)

More News

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...