Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Yi Barazanar Fara Yajin Aiki

Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta NARD tayi barazanar tsunduma yajin aiki matuƙar gwamnatin tarayya ta gaza biya bukatun kungiyar cikin makonni biyu.

NARD ta bayar da wa’adin ne a ƙarshen taron shugabanninta na kasa ranar Asabar a Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

Shugabannin kungiyar na kasa sun ce, gwamnatin tarayya taki yarda ta tattauna da kungiyar ko kuma ɗaukar wani kwakkwaran mataki kan kara albashin likitocin.

Har ila yau kungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da kin biyan likitocin ariyas na shekarun 2014,2015 da kuma 2016.

Kungiyar ta kuma yi allawadai da kudirin dokar hana likitoci fita kasar waje har sai sun yi aiki a kasar nan na tsawon shekaru 5.

More from this stream

Recomended